
Alfijr ta rawaito Ɗan Majalisar ya ya bayyana cewar, hankalina ya karkata ga wani shafin Twitter na bogi wanda ke yaɗa labaran ƙarya da sunana, don haka nake so in sanarda duniya cewa banida Twitter account.
Bayanin hakan ya fito ta Hannun wata takarda da makusancin a kafafen yada labarai nazifi Bala Dukawa ya sanyawa hannu

Banji daɗi ba sam bisa yanda wasu kafafen yaɗa labarai ke alaƙanta wancan account dani ba tare da sunyi bincike ba.
Ina kira ga kafafen yaɗa labarai da su himmatu wajen bayar da rahotanni sahihai da kuma tantance majiyoyinsu kafin buga wani labari, musamman a wannan zamani da ake yada labaran ƙarya.
Ina kuma ƙara jaddada cewa a halin yanzu na mayar da hankali sosai wajen yin ayyukan alkhairi don cika alƙawuran yakin neman zaɓe da kuma samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar yankina.
In Ji Engr. Sagir Koki Zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya, Kano Municipal
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇