Gwamna Ganduje Ya Yafewa Malaman Makaranta Bashi

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado ya yafe wa Malaman makaranta da suka shiga tsarin mallakar gidaje ta hanyar biya a hankali daga albashinsu, ragowar kuÉ—in da ba su gama biyan gwamnati ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau Litinin ta cikin jawabinsa na bikin ranar ma’aikata a taron da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Ya kuma yaba wa ɗaukacin ma’aikatan Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da mulki har tsawon shekaru 8.

Da yake gabatar da jawabi a taron, shugaban kungiyar Kwadago reshen Kano kwamared Kabiru Inuwa, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta hanzarta magance matsalolin da ƴan ƙwadago da kuma ƴan fansho ke fuskanta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *