
Alfijr ta rawaito Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ma’aikatan Najeriya zai basu albashi mai kyau tare da kula da hakkin su da bunƙasa tattalin arzikin su..
Ya ba da wannan tabbacin ne a yau Litinin a Abuja a sakon sa na goyon baya ga ma’aikatan Najeriya a bikin ranar ma’aikata ta duniya ta 2023.
Ya kara da cewa ma’aikata a kasar nan za su samu albashi ingantacce da za su samu rayuwa mai kyau da kuma wadata iyalansu a karkashin shugabancinsa.
Tinubu ya kuma tabbatar wa ma’aikatan Najeriya cewa shi abin dogara ne kuma abokin aiki a fafutukar tabbatar da adalci a zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin ƴan Nijeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ