Gobara Ta Tashi A Birnin Makkah Masu Umrah 8 Sun Mutu 6 Sun Jikkata

Alfijr ta rawaito wasu ƴan kasar Pakistan takwas a yayin da suke gudanar da aikin Umrah ƴan ƙasar Pakistan sun mutu, wasu shida kuma suka jikkata a wata gobara da ta tashi a wani otal da ke birnin Makkah.

Da yake tattaunawa da manema labarai kan faruwar lamarin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce, “muna da rahoton mutuwar ‘yan Pakistan takwas, shida kuma suka jikkata.

Ofishin Jakadancin mu na Jeddah na tuntubar hukumomin yankin, domin basu agajin gaggawa kan wadanda abin ya shafa da Iyalansu.

Rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a hawa na uku na otal din dake kan Ibrahim Khalil Road.

Wata majiya ta bayyana cewa Maniyyatan yan kasar Pakistan, Bangladesh, da sauran alhazan Umrah tuni suka fice daga otal din.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *