An Fara Ƙone Adaidaita Sahun Ƴan Fashin Waya A Kano

Alfijr ta rawaito cikin daren ranar Asabar wasu fusatattun matasa sun yi dirar mikiya kan ƴan fashin wayar a unguwar Kabuga dake birnin Kano, har suka ƙone Baburin adaidaita sahun ɗaya daga cikin yan Fashin waya.

Wani ganau ya shaidawa Alfijr cewar,  ƴan fashin wayar sun yi yunƙurin aikata fashin, inda matasan da za a yi wa fashin wayar suka nemi taimakon jama ar da ke kusa da wajen.

Sai dai waɗanda ake zargin da fashin wayar sun ranta a na kare dukansu , sun bar baburin adaidaita sahun da suke aikata laifin fashin wayoyin jama’a da shi.

Ganau din ya bayyana cewar jama’ar da ke wajen sun ƙone Baburin adaidaita sahun ƙurmus.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

2 Replies to “An Fara Ƙone Adaidaita Sahun Ƴan Fashin Waya A Kano

  1. Dama tsoron su da akeji yasa suke cin karensu ba babbaka, Alhamdulillah yanzu jamaa sun fara zasuyi wa kansu Magani…. Ya Allah ka karawa Bawa Al’umma karfin gwiwar kare kansu Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *