Gwamnatin Tarayya Ta Tumbuke Shugaban FAAN Ta Maye Gurbinsa Nan Take

Alfijr ta rawaito Gwamnatin tarayya ta kori manajan daraktan hukumar kula da filayen tashi da sauka da tashin jiragen sama na tarayyar Najeriya kaftin Rabiu Yadudu.

Hakazalika gwamnatin tarayya ta amince da nadin manajan kula da filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, Kabir Mohammed, a matsayin sabon Manajan Daraktan FAAN.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya nada shi a matsayin shugaban kwamitin aiwatar da taswirar sufurin jiragen sama a watan Janairun 2022, matsayin da ya hada da ofishinsa a matsayin Babban Manajan Ayyuka na Musamman a FAAN.

Mohammed kafin an nada shi a matsayin sabon shugaban FAAN ya kasance babban manajan yankin Arewa ta tsakiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Gwamnatin Tarayya Ta Tumbuke Shugaban FAAN Ta Maye Gurbinsa Nan Take”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *