
Alfijr ta rawaito fashewar wani shagon walda da ke karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu uku, ranar Lahadi da yamma.

Da yake ba da labarin yadda lamarin ya faru, wani mazaunin unguwar ya ce: “Lokacin da na ji karar fashewar wani abu mai karfi, abin da ya fado min shi ne ‘yan bindiga sun kai farmaki.
“Lokacin da na ga mutane suna gudu zuwa shagon walda inda fashewar ta faru ne hankalina ya kwanta cewa ba ‘yan bindiga ne suka afkawa ba. “Bayan bincike, an gaya min cewa fashewar ta fito ne daga wani shagon walda kuma an samu asarar rayuka da jikkata wasu da dama.”

Kazalika, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, da aka tuntube shi, ya tabbatar da cewa fashewar ta auku ne da yammacin ranar Lahadi.
PPRO ya bayyana adadin wadanda suka jikkata zuwa hudu.
Abubakar ya ce, “fashewar ba ta da alaka da kalubalen tsaro da ke addabar yankin, sai dai sakamakon fashewar wani silinda a shagon wani ma’aikacin walda da ke yankin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.
“Wasu uku da suka samu raunuka kuma suna cikin mawuyacin hali, suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba a jihar.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ