Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban EFCC Na Riko

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nada Abdulkarim Chukko a matsayin shugaban riko na hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa.

An nada shi ne kwana guda bayan dakatar da shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa wanda a yanzu haka yake hannun hukumar tsaro ta DSS bisa binciken da ake yi kan ayyukan ofishinsa.

Kafin nadin nasa, Abdulkarim Chukko shi ne daraktan gudanarwa na EFCC kuma yana cikin ma’aikatan da suka soma aiki a hukumar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *