Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar sa, Alhaja Abibatu Mogaji, shekaru 10 da rasuwa.
Shugaban ya wallafa hoton marigayiyar mahaifiyarsa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.
Ya yi la’akari da zaman da suka yi tare da irin kwazon aiki da tsayuwar daka da jajircewa da ta sanya a cikinsa, inda ya ce, “Shekaru 10 da suka wuce, a yau ne mahaifiyata mai suna Alhaja Abibatu Mogaji ta rasu.
A wannan rana, ina tunawa da soyayyarta, ɓacin rai, sadaukarwa, da karamcinta.
“Koyaushe zan kula da lokacin da muka yi tare da ƙimar aiki tuƙuru, gaskiya, da juriya da ta cusa a cikina.
Allah ya gafarta Mata tare da ci gaba da hutar da ranta.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
