Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Mai riƙon Shugabancin Hukumar Lura da Makarantun Sakandire ta jihar KSSMB Malam Ado Tumfafi. Da kuma Shugaban Kwalejin Lafiya ta Health Technology Bello Ɗalhatu,
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar.
Sanarwar ta zargi Tumfafi da karɓar kuɗin ɗalibai da sanya wa malamai harajin ba gaira ba dalili da sunan kuɗin fom ɗin ƙarin girma da sauran zarge zarge.
Gwamnatin ta kuma umarci manyan sakatarori na ma’aikatun ilimi da lafiya da su kafa kwamitin bincike a kan mutane biyun.
Hakazalika ya bayyana cewar gwamnatin Kano ta ce ba zata sassauta wa duk wani shugaban hukuma da ya yi amfani da ofishinsa wajen cuzgunawa jama’a ba gaira ba bu dalili ba.
Haka kuma ta yi alƙawarin ƙwato wa iyayen ɗalibai da Malamai da aka karɓi kuɗinsu da sauran haƙƙoƙinsu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Alhamdu lillah,tabarakallah
Gaskiya ne
Alhamdulillah, wan nan kafar sadarwa ta alfijir, labaranku yana kayatar dani Allah ya yi muku jagora, nine mai kau narku, Mal. Alh. Sabi’u. Nagode da damar da kuka bani
Ameen ameen dan uwa
Muna godiya da addu oinku