Hukumar Karbar Korafe-korafe Ta Kaddamar Da Bincike

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta kaddamar da fara bincike a hukumance kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan faifan bidiyon karɓar Dala

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wata ganawa da manema labarai yayin da yake tabbatar da kama wani tsohon kwamishinan jihar a zamanin mulkin Ganduje Injiniya Idris Wada Saleh.

Muhyi ya sha alwashin sake bude binciken Ganduje kan faifan bidiyon Dala da ake zargin tsohon gwamnan yana cusawa a aljihun rigar sa na kudaden dalar Amurka da ake zargin an karbo daga hannun ‘yan kwangila, zargin da tsohon gwamnan ya musanta.

Rimingado, ya bayyana cewa hukumar ta fara gudanar da bincike a hukumance kuma a halin yanzu tana nazarin rahotannin da suka shafi faifan bidiyo.

“Mun sake bude bincike a hukumance kuma mun shiga da kafar dama. Babu wani takamaiman umarnin kotu da ya hana mu matakan da muke dauka, wanda bincike ne sabanin yadda wasu ke son jama’a su yadda da shi,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta rubuta wasika zuwa ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC domin neman hadin gwiwa a binciken da kuma yiyuwar gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya.

Sai dai ba ta samu wani martani daga hukumar EFCC ba, amma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar tare da maraba da hukumar EFCC da sauran hukumomin bincike idan suka yanke shawarar hada kai da ita.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *