Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da gaggauta rabon kayan abinci a fadin kananan hukumomin 14 a matsayin kayan agaji saboda cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Alfijir Labarai ta rawaito a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ya jaddada cewa matakin raba kayan abinci ya yi daidai da yanayin da ake ciki a kasar nan da kuma kudirin gwamnatin jihar Zamfara na dakile illolin hauhawar farashin man fetur, ya ce gwamnatin jihar ta fitar da tsare-tsare don ganin cewa abin da ya dace ya isa ga talakawa ba tare da wani tangarda ba.
Ya kara cewa , Gwamnan ya amince da gaggauta rabon kayan abinci a matsayin abin da zai rage wahalhalun da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
“Kashi na daya na rabon abinci zai kunshi Shinkafa da Masara da sauransu, ya ce “An kafa kwamiti mai karfi da zai yi aiki bayan amincewar Gwamnan, wannan tsari zai kasance mai ban sha’awa kuma za a raba kayan abincin ga talakawa da marasa galihu a fadin jihar.
“Bugu da kari, gwamnati ta yi imanin cewa tallafin zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun da ke tattare da cire tallafin.