Gwamnatin Kano Ta Ware Miliyan 854, Don Aure Zawarawa Za Ta Kuma Gyaran Gadoji Uku

Hakan na kunshe ne cikin zaman da majalisar zartarwa ta gudanar a ranar laraba karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf

Majalisar zartarwa ta amince da abubuwa kamar haka:

1- Mun saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar Kano.

2- Na naɗa kwamiti na musamman da duba yadda zamu biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.

3- Za’a gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami’ar Bayero dake nan Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimi addini ta Malam Aminu Kano hadi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa’adatu Rimi. -AKY

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Gwamnatin Kano Ta Ware Miliyan 854, Don Aure Zawarawa Za Ta Kuma Gyaran Gadoji Uku”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *