Hakan na kunshe ne cikin zaman da majalisar zartarwa ta gudanar a ranar laraba karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf
Majalisar zartarwa ta amince da abubuwa kamar haka:
1- Mun saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar Kano.
2- Na naɗa kwamiti na musamman da duba yadda zamu biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.
3- Za’a gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami’ar Bayero dake nan Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimi addini ta Malam Aminu Kano hadi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa’adatu Rimi. -AKY
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Masha allah Ya Allah ka kar man basira