Gwamnan Kano Ya Naɗa Fauziyya D Sulaiman Mukamin SSA

Alfijir Labarai ta rawaito marubuci Fauziyya D Sulaiman ta wallafa haka a shafinta kamar haka

ABUN KAMAR DA WASA
Dazu wani ya kirani ya gaya mun suna meeting da mai girma Gwabnan Kano Abba Kabir Yusif, ya yi ta ambaton irin aikin da na ke yi saboda yana bibiyar shafina, ya ce tabbas kina abu mai kyau ki ci gaba na yi godiya
.
Da laasar kuma sai abokin aikina Nasir Nid ya shigo office yana dariya ya ce Uwar marayu mai girma gwamna ya baki mukami akan aikinki na jinkai, na ce tsokanata ka ke ya yi, ya yi ta rantsuwa muna dariya.

Zuwa can sai ga kiran Sunusi Oscar ya ce mun hajiya Fauziyya mai gurma Gwabna ya baki mukamin SSA, na ce ni kuma, ya ce eh yanzu haka muna meeting da shi zan kira ki idan mun kammala, zuwa can ya kira ya ce mu hadu.

Bayan mun hadu ya bani takardarnan ya ce mai girma Gwabna ne ya ce a baki, na rike baki da mamaki na ce ni da ba yar siyasa ba yaya zaa bani mukami, sai ya ce eh ai daman ba akan siyasa aka zabe ki ba, mai girma Gwamna ya baki mukami akan aikin da ki ke yi na tallafi da jinkai domin yana ganin aikinki yana bin fejinki hankalinsa yana tashi akan duk abun da ki ke sakawa, ga takardar ki amsa.

Na amshi takardar na kalla, na ce yanzu wannan daga hannun gwabna ta ke, ya ce kwarai kuwa duk Kano wa ya isa ya yi rubutu da jan biro idan ba gwabna na.

Kamar dai yadda ku ke ganin wannan takarda mai girma Gwamnan Kano ya bani mikamin SENIOR SPECIAL ASSISTANT NEEDY AND VULNERABLE, ina godiya kwarai da gaske ga mai Girma Gwamna.

Ina neman addu’ar ku bisa wannan nauyi da Mai girma Gwamna ya dora mun yan’uwa, Allah ya sa ya zama alkairi ga al’ummar jahar Kano, Allah ya bani ikon cinye jarrabawar da ke tattare da wannan nauyin Amin ya Allah.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Gwamnan Kano Ya Naɗa Fauziyya D Sulaiman Mukamin SSA”

  1. Alhamdulillah Masha Allahu Ina taya Fauziyya D Sulaiman murnar wannan mukami da Maigirma gwamna ya bata. Hakika ta cancanta. Allah ya tayata riko yasa ayi lafiya a gama lafiya,Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *