Lauyan Gwamnan Kano Ya Magantu Akan Daukaka Karar Da Aka Kora A Ranar Alhamis

Barasta Badamasi Sulaiman ya magantu kan daukaka karar da Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya shigar a abuja

Alfijir Labarai ta rawaito cewar an daukaka kara ne kan shigo da shedar Dr. Aminu Idris Harbau ba bisa ka’ida ba, musamman lokacin da ya kamata a shigo da shedar ta sa ya wuce kuma ba su nemi a tsawaita musu lokaci ba, a sakamakon haka ne gwamnan Kano ta hannun babban lauyan sa Chief Adegboyega Awomolo, SAN ya yi daukaka kara.

Ɗaukaka ya zo ne tun Kafin wannan shaida ya zo bada shaida, kuma bayan ya bada shaidar aka ga tafiya kotun ɗaukaka karar ma ba shi da wani amfani, ta yadda aka yi wasan kura da shaidar shi Dr. Aminu Harbau ɗin a wajen Cross Examination, ma’ana lokacin da lauyan gwamnan kano yake masa tambayoyi, yayi masa tambaya kamar haka:I Ya Bada Amsoshi Kamar Yadda Suke A Cikin Tambayoyin:

  1. A sakin layi na bakwai na shaidar ka, ka ce All People’s Congress ne suka ba ka aiki yace A’a All Progressive Congress ne bayan kuma a rubuce All People’s Congress ne.
  2. Ya tambaye shi duk wani Analysis hasashe, ba zai cika ba, sai an yi shi daidai, kuma babu san zuciya yace eh, sai yace masa tebur din ka na daya da na biyu total ɗin ba daidai ba ne yace a’a daidai ne, sai ya ba shi kalkuleta yace ka buga lissafin ka gani, ya buga ya kasa fadar amsa, sai lauyan yace masa kada ka bata mana lokaci, ka yarda lissafin ba daidai ba ne, yace eh ba daidai ba ne, to Kuma wane shiririta za ku zo kuna yi bayan an yi Discrediting ɗin shaidar na ku wanda ranar da aka fito sai da suka ji kamar su yi masa dukan tsiya.
  3. Ya kuma tambaye shi kai ma aikacin gwamnati ne, yace eh, sai yace da Izinin wanda suka dauke ka aiki kazo bada bada shaida yaya aa.
  4. An tambaye shi wannan lissafin da ka yi babu wani abu na musamman a ciki tunda ko su alkalan nan guda uku aka aka bawa aikin warewar da lissafawaza su iya? Yace eh.

Kamar yadda mai bawa gwamna shawara Salisu Yahaya Hotoro ya wallafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Lauyan Gwamnan Kano Ya Magantu Akan Daukaka Karar Da Aka Kora A Ranar Alhamis”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *