Sojojin Nijar Sun Katse Wuta Da Ruwa A Ofishin Jakadancin Faransa

Duk hukumar da aka gano tana bai wa ofishin jakadancin Faransa wadannan abubuwa, za a dauke ta a matsayin “makiyiyar al’umma,”

Alfijir Labarai ta rawaito sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun katse wutar lantarki da ruwa na ofishin jakadancin Faransa da ke kasar, sannan sun hana a kai abinci cikinsa, a cewar rahotanni da dama.

Sojojin sun dauki irin wannan mataki a ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Zinder, kamar yadda rahotanni suka bayyana ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin kasa da ke goyon bayan sojojin mai suna National Support Committee for the National Council for the Safeguarding of the Country (CNSP), Elh Issa Hassoumi Boureima, ya bukaci dukkan hukumomin da ke bayar da ruwa da wutar lantarki da abinci su daina bai wa ofishin jakadancin na Faransa, a cewar rahotanni.

Hakazalika, duk hukumar da aka gano tana bai wa ofishin jakadancin Faransa wadannan abubuwa, za a dauke ta a matsayin “makiyiyar al’umma,” in ji rahotanni.

Rahotannin na zuwa ne bayan wa’adin da sojojin suka bai wa jakadan Faransa da ke kasar na awa 48 ya cika ranar Lahadi.

Sojojin na Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fice daga kasar cikin awa 48 a yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan jiya.

Nijar ta fada cikin rikici ranar 26 ga watan Yuli bayan Janar Abdourahamane Tiani, wani tsohon shugaban sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar, ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum.

Bayan nan ne Faransa da wasu kasashen Yamma suka soma kwashe ‘ya’yansu daga Nijar.

TRT Afrika

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Sojojin Nijar Sun Katse Wuta Da Ruwa A Ofishin Jakadancin Faransa”

  1. Right ! Better Niger and All African countries to fight colonialism and neo-colonialism to gain sovereignty and our independence both politically, socially, economically, at’el.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *