Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya Magantu Akan Shari’ar Zabe

ƙara samun ƙwarin guiwar yin aiki ga ƙasa tuƙuru ba tare da nuna bambanci, ɓangaranci, ƙabilanci, addinanci ko nuna fifiko ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga masu jayayya da shi a kotu cewa, tunda an sake jaddada nasara a kan sa, to su haƙura, a rungumi kishin ƙasa tare da su da magoya bayan su baki ɗaya.

Cikin sanarwar Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar bayan yanke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi fatali da ƙarar da abokan hamayya su ka shigar, Tinubu ya ce ya ƙara samun ƙwarin guiwar yin aiki ga ƙasa tuƙuru ba tare da nuna bambanci, ɓangaranci, ƙabilanci, addinanci ko nuna fifiko ba.

Ya ce babban muradin sa shi ne ciyar da Najeriya gaba da kuma kare dimokraɗiyya.

Hakan na zuwa ne bayan da Kotun Shari’ar zaben mai alƙalai biyar a ƙarƙashin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta yi fatali da ƙararrakin da Atiku, Obi, LP da APM su ka shigar, bisa dalilin cewa sun kasa gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da za ta tabbatar da maguɗin da su ke zargin an tafka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *