Ta addanci: Wani Mutum Ya Sassari Limamin Coci Da Adda Ya Kashe

Ya kasance matashi mai shekaru 20, da isarmu sai ya yi mana barazana cewa idan muka kuskura muka hau benen da dakin Paston yake zai kashe mu.

Alfijir Labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa wani mutum da ake zargin ya kaiwa Fasto Sagie hari da adduna a garin Sapele na jihar Delta a ranar Alhamis.

Malamin mai shekaru 60 a duniya yana hutawa ne a cikin dakin kwanansa da ke yankin bututun mai na titin MTN, inda maharin ya kutsa cikin gidansa tare da yi wa ‘ya’yansa guda biyu masu shekaru 8 da 11 barazana.

Yaran da suka firgita suka fice daga gidan suna ihu don neman taimako.

Wata majiya da ta yi ikirarin cewa tana cikin wadanda suka kai gawar Fasto Sagie dakin ajiye gawa da kuma makwabcinsa, ta shaida wa Vanguard cewa sun ji yaran suna kururuwar cewa wani ya kutsa cikin gidansu, inda ya far wa mahaifinsu sara da adduna.

Majiyar ta ce, “Mun fito da gudu muka ga maharin.

Ya kasance matashi mai shekaru 20, da isarmu sai ya yi mana barazana cewa idan muka kuskura muka hau benen da dakin Paston yake zai kashe mu.

Daga bisani ya yi tsalle daga ginin bene ya gudu.”

Majiyar ta kara da cewa yayan marigayin sun bayyana maharin dan cocin su ne.

“Yaran sun gaya mana cewa shi dan cocin su ne kuma sun gane shi, har ma sun bayyana inda yake zaune,” inji majiyar.

An bayyana cewa Fasto Sagie ya sami raunuka sosai a kansa kuma ya mutu akan hanyar zuwa asibiti.

Wani makwabcinsa mai suna Isaac ya ce, “Ya ja numfashi na karshe a hanyar zuwa asibiti inda motarsa ta lalace.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *