A daren jiya Asabar ne ƴan bindiga suka kai hari Gidan Wakilin Nufawan Tafa Alh Mohammed Makusidi dake Garin Sabon Wuse a Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja inda suka ringa yiwa gidan ruwan harsashai.
Alfijir Labarai ta rawaito wani makwafcin Sarkin Nufawan ya bayyanawa wakilin mu cewa, a yayin da Magidanci ya buɗe kofa ne ya shammace su ya halbi daya daga cikin ƴan bindigan wanda nan take ya fadi, Sannan ya samu daya a kafa wanda daga baya aka gano wani makwafcin sa ne dake kiwon shanu kusa da gidan sa.
A makon daya gabata a ranar Asabar ƴan bindiga sun kai hari gidan shugaban karamar hukumar ta Tafa in da nan ma basu sha da dadi ba.
Har izuwa yanzun dai babu wata sanarwar daga hukumomin tsaro ko bangaren Gwamnati dangane da harin.
Tsalle Daya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb