Daga Baba Usman Gama
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Chidoka Osita, ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sauka daga kan mukaminsa a mutunce saboda zargin badakalar takardun karatunsa.
Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka, ta ce ba ta da takardar shaidar karatu da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kafin zaben 2023.
Atiku ya buƙaci Kwankwaso da Peter Obi su haɗa hannu da shi wajen binciken Tinubu.
Layin motoci da babura sun dawo gidajen mai, farashi ya na cigaba da tashi a kowace rana.
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya bayyana cewa ba a biya ko sisi ba kafin sakin kwamishinan watsa labarai na jihar da aka sace.
Kotun soja a Najeriya ta samu wani janar da laifin sace miliyoyin nairori.
Kotun zaɓen gwamnan jihar Kebbi, ta tabbatar da nasarar gwamna Nasir Idris na APC.
Jami’ar Abuja ta sanya gwajin shan Æ™waya a matsayin sharaÉ—in ba da damar karatu
Wata daliba Æ´ar shekara 10 mai suna Rofiat ta rasa ranta bayan da wata mota ta tunkuÉ—e ta a harabar makarantarsu mai suna Isiu Grammar School da ke unguwar Ikorodu a jihar Legas.
Sojin Somalia sun kashe mayakan al-Shabaab 55 a wata arangama tsakaninsu.
Pakistan za ta kori ‘yan gudun hijirar Afghanistan miliyan 1 da dubu 300.
Shugaban mulkin sojan Burkina Faso ya kori shugaban rundunar jandarmomi.
Rukunin farko na dakarun Faransa za su fara ficewa daga Nijar a yau Alhamis.
Kudin samun izinin sayen mota a Singapore ya kai kimanin naira miliyan 80.
Saudiya ta mika bukatar daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2034.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb