Kotun Sojoji Ta Yankewa Manjo Janar Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari

Screenshot 20231010 202701 com.android.chrome edit 14351829895204

An gurfanar da Mohammed ne a kan tuhume-tuhume 18 da suka hada da jabun takardu, karkatar da kudade, da kuma hada baki da sauransu.

Alfijir Labarai ta rawaito kotun sojin Najeriya da ke zamanta a Abuja, ta yanke wa tsohon Manajan Darakta na rukunin, Nigerian Army Properties Limited, Manjo Janar Umaru Mohammed, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari a ranar Talata.

Hakazalika kotun ta umarce shi da ya mayar da tsabar kudi dala 2,178,900 da kuma Naira biliyan N1.65bn ga kadarorin Sojoji da NAPL.

An gurfanar da Mohammed ne a kan tuhume-tuhume 18 da suka hada da jabun takardu, karkatar da kudade, da kuma hada baki da sauransu.

Ko da yake manjo Janar din ya ki amsa dukkan zarge-zargen, amma kotun ta same shi da laifuka 14.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *