An dauki mutum goma-goma daga kananan hukumomi biyar na jihar.
Alfijir Labarai ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta yaye tubabbun ‘yan daba 50 wadanda suka samu mukamin kwansitabul na ‘yan sanda.
A wata sanarwa da kakakin ƴan sanda Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Litinin, ya ce mutanen na cikin ‘yan daba 222 da suka yi saranda ga ‘yan sanda tare da daukar alkawarin ba za su sake aikata laifi ba.
“Yau rana ce ta farin ciki ga jama’ar Kano da ‘yan sandan Kano saboda mun yaye matasa 50 daga cikin 222 wadanda suka tuba daga daba wadanda tuni suka yi alkawarin ba za su sake yin daba ko wani abu da zai kawo rashin zaman lafiya a jihar ba,” in ji CP Mohammed Usaini Gumel.
An dauki mutum goma daga kananan hukumomin Dala da Fagge da Ungogo da Municipal da kuma Gwale har suka zama mutum 50.
Gumel bayyana cewa sabbin ma’aikatan sun samu horo na watanni biyu kafin suka samun mukamin kwansitabul din.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo