Amurka ta saka sojojinta 2,000 a shirin ko-ta-kwana kan rikicin Gaza da Isra’ila

Screenshot 20231017 151553

Rundunar sojin Amurka ta saka sojoji 2,000 a shirin ko-ta-kwana a daidai lokacin da ake kara samun rikici tsakanin Isra’ila da Hamas.

Alfijir Labarai ta rawaito Hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon ce ta tabbatar da hakan a Talata.

Kafofin watsa labaran Amurka sun bayyana cewa dakarun ko sun je can za su bayar da tallafin kiwon lafiya ne da kuma kawar da bama-bamai.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai tafi Isra’ila a ranar Laraba domin nuna goyon bayan Amurka ga babbar kawar kasar wato Isra’ila.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan cewa matsalar karancin abinci na kara karuwa a Zirin Gaza da Isra’ila ta yi wa kawanya.

Shirin na WFP ya bayyana cewa a halin yanzu abincin kwanaki hudu zuwa biyar ya rage a shaguna.

WFP din ya ce kayayyaki na kara raguwa a manyan dakunan ajiye kayayyaki da ke cikin Falasdinu amma lamarin ya fi kamari a shaguna.

Shirin na WFP ya ce cikin gidajen burodi 23 da ya bai wa kwangila biyar ne kacal ke iya aiki.

Sarki Abdullah II na Jordan ya gana da Shugaban Gwamnatin Jamus OIaf Scholz a Berlin inda ya ce kasarsa da kuma kasar Masar ba za su amince su karbi duk wani dan gudun hijira na Falasdinawa ba.

“Dole a shawo kan wannan lamari a cikin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan,” in ji shi. “Kuma bai kamata wasu su dauki alhakin wannan batu ba.”

Kazalika Abdullah ya ce ya kamata a dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin an kauce wa ta’azzarar yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

“Gaba daya yankin yana fuskantar bala’i,” in ji Abdullah. “Wannan sabon rikicin zai iya kai wa ga wargajewarmu.”

TRF Afirka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *