Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata, ya bayar da umarnin rusa gidajen karuwai da masu aikata laifuka da suka yi kaurin suna wajen karuwanci, ’yan daba da sauran miyagun ayyukan cikin sa’o’i 72.
Alfijir Labarai ta rawaito Zulum ya ba da umarnin ne a wata ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru a ‘Bayan Quarters’, wani matsugunin da ke kusa da rukunin gidajen ma’aikatan jirgin kasa, a Maiduguri.
Yankin yana ɗaukar ƴan daba, ayyukan aikata laifuka da ƙananan yara don karuwanci na kasuwanci.
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun yawaitar ayyukan ta’addanci da ke da alaka da wadannan haramtattun gidajen karuwai da wuraren aikata laifuka da suka hada da karuwanci da safarar miyagun kwayoyi da sauran ayyukan haram.
Ya kara da cewa, wadannan ayyuka ba wai barazana ce ga tsaron jihar kadai ba, har ma suna haifar da munanan dabi’u da ke lalata rayuwar al’umma da kuma mutuncin daidaikun mutane da lamarin ya shafa.
Zulum ya bayyana cewa, yayin da za a rushe matsugunin da ke dauke da masu aikata laifuka da kananan yara mata domin yin lalata a cikin sa’o’i 72, dama gidajen karuwai ba bisa ka’ida ba, Gwamnan ya bada awanni 12 su fice daga yankin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo