Majalisar Zartaswar Najeriya ta amince da kafa Asusun Magance Talauci a kasar

๐Ÿ“ธ Villa

Edu ya ce โ€œA yau Majalisar ta amince da kafa asusun tallafawa jin kai da fatara da talauci wanda zai kasance karkashin hukumar gudanarwar Kwamitin

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin kafa Asusun tallafawa Jamaโ€™a don kawar da Talauci da za a rika fitar da dala Biliyan 5 duk shekara domin tafiyar da shirin.

Amincewa da kudurin kafa Asusun na zuwa ne a taron Majalisar zartarwa ta Tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya Jagoranta a ranar Litinin a fadar Shugaban.

A cewar Ministar harkokin jin ฦ™ai da rage radadin talauci Dakta Betta Edu, kuษ—aษ—en za su taimaka sosai wajen fuskantar duk wani yanayi na gaggawa a kasar.

Ministan Kuษ—i da Haษ—in Kan Tattalin Arziki Wale Edun da sauran Ministoci sun kasance tare da su a cikin hukumar don sauฦ™aฦ™e ayyukanta na Musamman na tara kuษ—aษ—e daga ฦ™ungiyoyi masu ba da tallafi.

Edu ya ce โ€œA yau Majalisar ta amince da kafa asusun tallafawa jin kai da fatara da talauci wanda zai kasance karkashin hukumar gudanarwar Kwamitin, sannan kuma ba shakka Mambobin kwamitin za su yi aiki da shi a tsanake wajen aiwatar da wannan asusun na jin kai da fatara.

Tabbas zai haษ—a da Ministan Kuษ—i da Haษ—in Kan Tattalin Arziki ciki har da sauran Ministocin da suka dace da tsarin.

Wannan wani nauโ€™i ne mai sassaucin raโ€™ayi na samar da kuษ—aษ—e, wanda ya kamata ya taimaka wa Najeriya yadda ya dace don magance rikice-rikice da kalubale da kuma magance matsalar talauci a Najeriya yadda ya kamata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai ๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *