Tun da safe, an ta kai hare-hare mita 50 daga asibitin,” a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin X.
Alfijir Labarai ta rawaito majalisar dinkin duniya tace a ranar lahadin nan dubban mutane sun fasa dakunan ajiyar kayayyakin agaji na Majalisar da ke Gaza.
Majalisar ta ce mutanen sun kwashi fulawa da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.
Thomas White wanda darakta ne a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce fasa dakunan ajiyar wata alama ce da ke nuna doka da oda ta soma yankewa sakamakon matsi da jama’a ke ciki.
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyana hukumomin Isra’ila sun mata babbar barazana kan cewa su tattara su bar asibitin Al Quds da ke Gaza sakamakon suna da niyyar kai masa hari.
“Tun da safe, an ta kai hare-hare mita 50 daga asibitin,” a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin X.
Isra’ila ta kai hari kusa da asibiti mafi girma da ke Gaza, kamar yadda mazauna suka tabbatar.
Mazaunan sun ce harin da Isra’ila ta kai ya lalata hanyoyin da za su kai ga asibitin, wanda asibitin ya kasance wata mafaka ga dumbin Falasdinawa da ke guje wa hare-haren Isra’ila.
Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ilar ke ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp