‘Yan kasuwar Man fetur sun bayyana cewa, Farashin man zai iya komawa Naira 700 zuwa 800 kan kowace lita.
Alfijir Labarai ta rawaito ƴan kasuwar Fetur ɗin sun bayyana dalilin su cewar, matsalar karancin dalar amurka wadda da itace ‘yan kasuwar ke amfani suke shigo da man fetur din daga kasar waje.
Hakanan kuma ‘yan kasuwar sun koka da cewa gwamnati ta dawo da kayyade farashin man fetur din a fakaice.
Daya daga cikin shuwagabannin ‘yan kasuwar, Mrs. Adenike Labanjo tace kamfanin man fetur na kasa, NNPC ne kadai ke samun dalar shigo da man fetur din daga kasar waje
Tace kuma babu wanda zai iya gasa dashi.
Shima daya daga cikin ‘yan kasuwar daga Arewa, Dr Mohammed Salaudeen ya bayyana cewa yanzu idan mutum zai sayi tan 10,000 na man fetur din sai yana da Naira biliyan 7 wanda a baya rabin kudinne ake amfani dasu wajan sayen man fetur din.
Yace kuma kusan kaso 90 na masu depot din sayar da mai masu zaman kansu na Najeriya sun kulle saboda ba zasu iya ba.
Liberty TVR
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp