Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Asabar 04/11/2023 – 20/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya bayyana yadda ya sanya shugabannin ƙungiyar ECOWAS, shawo kan fushinsu kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Tinubu ya gode wa Faransa a kan dawo wa Najeriya $150m da Abacha ya ‘sace’.

Gwamnan Zamfara ya karɓi kayan agajin gaggawa na al’ummar jihar Zamfara waɗan da lamarin yan bindiga ya shafa.

Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wasu mutane 2 da laifin satar wata babbar motar kamfanin siminti ta Dangote da ke Ibese.

Majiyoyi a Legas sun tabbatar wa wakilinmu cewa an canzar da kowacce Dala daga tsakanin N750 zuwa N800 da safe, kafin ta kai N950 zuwa yamma.

Aƙalla fasinjoji 11 ne suka mutu inda wasu 10 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Jam’iyyar LP ta tsayar da dan takarar jam’iyyar PDP Dino Melaye amatsyin dan takararta a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi.

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jihar Abia a zaben da aka gudanar a watan Maris.

Hukumar EFCC ta samu izini daga kotu na kamo wani dan kasuwa da ta ke zarginsa da zambar naira biliyan hudu da miliyan dari takwas a Legas.

Sojoji sun samu nasarar halaka ƴan bindiga bakwai a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da kamfanin MultiChoice ya sanar cewa ya kara kudin kallo na tashoshin DSTV da GOTV.

Ba za a amince da aniyar Isra’ila ta kai wa ‘yan jarida hari ba: Daraktan Sadarwa na Turkiyya Altun.

Kamaru ta kulla yarjejeniya da Jamus kan noman auduga.

Faransa na goyon bayan ECOWAS wajen dawo da dimukaradiya a yammacin Afrika.

Girgizar ƙasa ta kashe mutane fiye da 100 a Nepal.

Ten Hag yace yana da yaƙinin ‘yan wasansu za su farfaɗo da United.

Saudiyya ta naɗa Yaya Toure mataimakin kocinta

Mainz ta soke kwantiragin El-Ghazi kan goyon bayan falasɗinawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *