INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023 bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.
Alfijir Labarai ta rawaito Kotun daukaka kara ta Kano dake zamanta a Abuja, ta sanya ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, 2023, domin sauraren karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar na kalubalantar soke zabensa da kotun sauraron kararrakin zabe ta Kano ta yi.
Sanarwar ta nuna cewa za a saurari karar mai lamba: CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 a ranar da aka fada.
Jam’iyyun da ke cikin karar sun hada da Gwamna Yusuf da jam’iyyarsa ta New Nigeria Peoples Party (NNPP) da kuma jam’iyyar adawa ta APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Idan za a iya tunawa, a ranar 20 ga watan Satumba, 2023, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta soke zaben gwamnan Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana cewa kuri’u 165,663 ba su da inganci, inda ta ce ba INEC ta sanya wa hannu ko tambari ba.
INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023 bayan ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.
Sai dai bayan da kotun ta cire kuri’u 165,663 daga cikin kuri’u 165,663, an rage kuri’unsa zuwa 853, 939, wadanda suka haura kuri’u 30,000 kasa da kuri’u 890,705 da Gawuna ya samu.
Sakamakon haka, kotun ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna tare da umurci hukumar zabe ta INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe na Mista Yusuf tare da baiwa Gawuna sabon.
Sai dai Mista Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP da kuma INEC sun daukaka kara kan hukuncin kotun.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp