Wata Sabuwa! Za a Kori Ƴan Keke-NAPEP Yan Adaidaita Sahu Daga Garin Abuja

Adaidaita Sahu

Wike ya ce daga watan Disamba sabbin motocin daukar mutane a kwaryar birnin Abuja za su fara aiki

Alfijir Labarai ta rawaito ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Disamba mai kamawa za a haramta ayyukan baburan Keke-NAPEP a garin Abuja.

Wike ya ce shirye-shirye sun yi nisa domin fito da sabbin motocin daukar mutane a kwaryar birnin Abuja daga wata mai zuwan.

Ya ce da zarar motocin gwamnatin sun fara aiki za a bukaci masu Keke-NAPEP su koma kauyukan Abuja da aiki.

“Na san yanzu matuka Keke-NAPEP za su fara cewa an toshe musu hanyar neman kudi, to amma dole mu dakatar da su domin inganta birnin Abuja, da samar da cikakken tsaro a birnin,” in ji ministan.

Wike ya bayyana hakan ne ranar talata, lokacin da yake ganawa ta musamman da masu tsara taswira da gina gidaje a Abuja, inda ya ce hakan zai rage matsalar tsaro a birnin.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Ina tabbatar muku idan motocin mu suka fara aiki matsalar kwace a cikin motocin haya za ta kau.

“Motocinmu za su rika zirga-zirga ne a hanyoyin Maitama, Asokoro da sauran sassan kwaryar birnin Abuja” inji Ministan Abuja.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *