Ƴan bindiga sun fasa gidan yari, sun kuɓutar da fursunoni

Gidan Gyaran Hali

Ƴan bindiga a yankin Amhara na Habasha mai fama da rikice-rikice sun fasa wani gidan yari tare da kuɓutar da ɗaruruwan fursunoni, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a garin Woldiya da ke arewacin Amhara a ranar Alhamis da dare.

Mazauna yankin, sun kiyasta cewa fursunonin da ke cikin gidan yarin sun tasamma ɗaruruwa, inda kuma aka kuɓutar da dukkansu bayan harin da ƴan bindigar suka kai.

Daga baya an sake kama gomman fursunonin da aka kuɓutar, sai dai har yanzu ana ci gaba da neman da yawa daga cikinsu.

An yi imanin cewa wasu daga cikin fursunonin mambobin ƙungiyar mayaka ta Fano ne da ke ci gaba da faɗa da dakarun gwamnati tun watan Agusta, inda wasu kuma suka kasance mambobin ƙungiyar ƴan sa kai wadda gwamnatin tarayya ta yanke shawarar rutsawa a watan Afrilu.

Matakin rutsa ƙungiyar da aka fi sani da ASF, ya janyo ce-ce-ku-ce, inda da yawa daga cikin mazauna yankin suka ce matakin kai kara sanya su cikin barazanar fuskantar hare-hare daga yankunan makwabta.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Babu wata sanarwa daga gwamnati kawo yanzu.

Faɗa ya ɓarke a watan Agusta kuma tun lokacin yankin Amhara ke cikin dokar ta-ɓaci.

An yanke hanyoyin intanet, abin da ya janyo wahala wajen samun ainihin bayanai kan abin da ke faruwa game da rikicin.

An kuma ruwaito ɓarkewar faɗa a ranar Alhamis kusa da birnin Lalibela, wuri mai daɗadɗen tarihi gine-ginen majami’u masu tsawon shekaru 900.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *