Jami’an Kwastam sun kama albarusai 975 da aka boye cikin buhanan shinkafa da aka yi fasa-kwauri zuwa Najeriya daga kasar waje.
Alfijir labarai ta rawaito Jami’an da ke aiki a Jihar Ogun ne suka kama wadannan albarusai a huhunan shinkafa biyar kan hanyar Palace/Ayetoro a Karamar Hukumar Imeko Afon.
Kwanturolan Kwastam na yankin, Ahmadu Shuaibu, ya ce sun kama makaman ne bayan masu fasa-kwaurinsu sun yi kokarin wucewa da su ta barauniyar hanya.
Ya kara da cewa bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu fasa-kwaurin makamai zuwa Najeriya ne a ranar Litinin suka kama albarusan.
A cewarsa, ana ci gaba da bincike domin kamo masu hannu wajen fasa-kwaurin makaman domin su fuskanci hukunci.
Jami’in ya bayyana fasa-kwaurin makamai a matsayin babban hadari da ke taimaka wa ayyukan ta’addanci da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp