Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Talata 26/12/2023 – 12/06/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai tare da yin alƙawari daukar mataki kan kisan gilla da ’yan bindiga suka yi wa mutane fiye da 140 a kauyukan Jihar Filato.

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa 19, ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai kan wasu al’ummomi a jihar Filato da suka yi sanadin mutuwar mutum sama da 140.

Sojin sama sun lalata haramtattun wuraren tace mai shida a Fatakwal.

Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yari a jihar Ogun.

Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya koka kan cewa ƴan ta’adda sun shafe shekara biyar suna mamaye makarantu a ƙaramar hukumar Barkin-Ladi ba tare da an tarwatsa su ba.

Zanga zangar kin jinin yaki ta barke ana tsakiyar wasa a birnin Milan na kasar Italiya, an rika daga tutar Falasdinawa yayin da ake kiraye-kirayen daina kai hare-haren bama-bamai a fadin duniya

Gobara tayi mummunar barna a kasuwar garin Gwarzo da ke Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Gwamnan jihar Niger, ya saka dokar haramta sha da sayar da barasa a wasu kananan hukumomin jihar.

’Yan Bindiga bindiga sun kona wata uwa da ’ya’yanta biyu tare da matar danta da ransu a Jihar Sakkwato.

’Yan sanda a Adamawa sun tabbatar da mutuwar mutum biyu ranar Kirsimeti a harin da aka kai yankin Kwapre a Karamar Hukumar Hong ta jihar.

Mutum 4 sun mutu wasu 59 sun ji rauni bayan wata tirela mai da ke dauke da mutane 73 da kaya ta yi hatsari hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An gudanar da bikin mafarauta na shekara shekara a Karamar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa.

NDLEA ta kama haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 1,458.709, da masu laifi 103 a Kaduna.

An samu fashewar wani abu a kusa da ofishin jakadancin Isra’ila a Delhi kasar India.

Ana neman wani uba bayan an gano gawar mata da ‘ya’yanta huɗu a Faransa.

Rasha ta tabbatar da lalata mata jirgin yaƙi a Tekun Bahar Aswad.

Gwamnatin sojin ƙasar Nijar ta ƙaryata labarin da wasu kafofin yada labarai suka yi cewa sun ayyana wa’adin da za su yi kafin mika mulki ga farar hula.

EPL: Nottm Forest ta sami nasara akan Newcastle da ci 3:1 a wasan yau.

EPL: Bournemouth ta sami nasara akan Fulham da ci 3:0 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *