Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima Ya Kaddamar da Ofishin Gwamnan Kano da aka sabunta

IMG 20231227 224937

Ina taya Gwamna Yusuf da ‘yan majalisar zartarwa murna saboda kyakkyawan aiki,” in ji mataimakin shugaban.

Alfijir labarai ta rawaito a ranar Laraba mataimakin shugaban kasa, Kassim Shettima ya kaddamar da ginin ofishin gwamnan Kano da aka yi wa kwaskwarima a gidan gwamnati da ke Kano.

Gine-ginen ya haɗa da ɗakin majalisa da aka sake fasalin, zauren taro na zartarwa na musamman

An samar da wannan ginin ne tun tsohon shugaban mulkin soja na farko a jihar, marigayi kwamishinan ‘yan sanda Audu Bako a shekarar 1967.

Gwamna Abba Yusuf ne ya taimaka wa mataimakin shugaban kasa; Kakakin majalisar wakilai, Dr Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sen. Barau Jibril; Sen. Kawu Sumaila da Mataimakin Gwamna Aminu Gwarzo wajen kaddamarwar.

Shettima ya yaba da jajircewar da Gwamna Abba Yusuf ya nuna na ganin an aiwatar da aikin a kan lokaci.

Ya bayyana cewa gyaran ofishin gwamnan zuwa yanayin zamani zai samar da kyakkyawan yanayi na aiki ga gwamnoni da ma’aikatan da suka gaje su su yi aiki yadda ya kamata.

“Ina taya Gwamna Yusuf da ‘yan majalisar zartarwa murna saboda kyakkyawan aiki,” in ji mataimakin shugaban.

(NAN)

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *