Jerin ma’aikatun da ke da mafi girman kasafin kudin shekarar 2024

IMG 20231231 103804

Ma’aikatar tsaro ta samu kaso mafi tsoka – N1.3tn a cikin kasafin shekarar 2024 da aka amince da shi.

Alfijir labarai ta ruwaito a ranar Asabar din da ta gabata ne, an samu karin kudirin kasafin kudi daga majalisun dokokin kasar biyu.

Majalisar ta kara kasafin kudin da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudi naira tiriliyan 1.2.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abubakar Bichi, ya shaida wa manema labarai a karshen zaman na musamman a ranar Asabar din da ta gabata cewa, an samu karin Naira tiriliyan 1.2 ne saboda hauhawar farashin kayayyaki, da kuma alkawarin da Kamfanonin Gwamnati, GOEs suka yi na kara musu kudaden shiga. .

A cikin kasafin kudin da aka amince da shi, ma’aikatar tsaro ta samu kaso mafi tsoka na N1.3tn.

Sannan kuma ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta biyo ta da N869.121bn.

Ma’aikatar ilimi ta samu N857.134bn.

Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a – N667.577bn.

Ma’aikatar Cikin Gida – N362.552bn.

Ma’aikatar Matasa – N201.467bn.

Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro – N199.763bn.

Ma’aikatar Harkokin Waje – N140.456bn.

Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci – N110.248bn.

Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya – N100.248bn.

Fadar Shugaban Kasa – N97.913bn.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *