Lamarin dai ya faru ne a daren lahadi 31 ga Watan Disamba, an shaidi matashin Ladanin mai suna Muhammadu Sani (Baha) a matsayun mutumin kirki, kuma shine ma ya ja sallar magriba a masallacin da yake ladanci a kasuwar Kurmi ‘yan kaji.
Alfijir labarai ta rawaito Muhammad Sani ya gamu da ajalin sa ne, sakamakon kisan gilla da wannan matashi ya yi masa.
Wasu sun bayyana yadda lamarin ya samo asali, kwanakin baya shi wannan yaron suna shaye-shaye a kofar gidan marigayin sai ya yi musu magana cewa “su daina yi musu shaye-shaye a wurin” ashe shi yaron ya Æ™ullaci Ladanin, shine jiya bayan marigayin ya ja sallar Magriba an idar, sai ya É—auki robobin ruwa guda biyu da ya É—ebo a famfo zai kai gidan sa, ashe makashin yana laÉ“e a kofar gidan da wùķa a hannun sa, yana Æ™arasowa É—auke da jarkokin ruwa kawai sai yaron ya zaro wuka ya caka masa, kafin jama’a su ankara ya gudu.
Nan marigayini ya shiga gida yana dafe cikin, jini yana ɗibar sa, kafin wani lokaci Allah ya karɓi ransa.
An yi Jana idarsa a dazu kamar yadda addinin muslumci ya tanadar.
Za muji ta bakin jami an tsaro kan lamarin

Dokin karfe
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a



https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl