Tinubu Ya dakatar da shugaba kuma ko’odineta ta hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa (NSIPA) Halima Shehu na wani dan lokaci daga mukaminta
Alfijir labarai ta rawaito Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dakatarwar da aka yi a gidan talabijin na kasa a hukumance a wani shiri kai tsaye a ranar Talata, 2 ga watan Janairu.
Har yanzu ba a tantance takamaiman musabbabin dakatar da ita ba, duba da nadin da aka yi mata watanni kadan da suka gabata
Sai dai wata majiya na cewa shugaba Tinubu ya dakatar da shugabar ne bisa zargin zamba a hukumar.
An ce mata ta sauka daga mukaminta domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake mata.
A halin yanzu, shugaban kasar ya nada Mista Akindele Egbuwalo a matsayin kodinetan riko na NSIPA, har sai an kammala cikakken binciken da shugaba Tinubu ya bayar.
Ya zuwa yanzu, shi ne kodinetan shirin N-Power na kasa, kuma sabon nadin nasa ya fara aiki nan take.
Tinubu ya nada Halima Shehu a watan Oktoba 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin nata a ranar 18 ga Oktoba, 2023.
Ta yi aiki a matsayin mai kula da shirin Cash transfer na ƙasa, inda ta yi amfani da ƙwarewar aikinta na banki da aikinta don ganin an daidaita shirin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl