Kotun ƙoli ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato.
Mutfwang na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 525,299 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda da ya samu ƙuri’u 481,370 a zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a Jos, babban birnin jihar ya tabbatar da zaɓen gwamna Mutfwang.
Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a Abuja a nata hukuncin ranar 19 ga watan Nuwamban bara ta soke nasarar Mr Mutfwang lamarin da ya sa gwamnan ya garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara da nufin ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl