Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 01/07/1445AH -13/01/2024

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya dakatar da shirin N-Power da dukkan shirye shiryen rage radadin talauci da ake gabatarwa Hukumar (NSIPA)

Shugaba Tinubu ya naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Kasa.

‘Yan bindiga sun jikkata mutum biyu suka sace wasu makiyaya shida a wani garin Fulani da ke Laying-Jirgi a Jihar Kaduna.

Matatar mai ta Dangote ta fara aiki.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya yi kiran haɗin kan ɓangaren adawar jihar domin ginawa da ciyar da jihar gaba.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yaba da hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta yanke da ya tabbatar da nasararsa.

Jam’iyyar APC ta yabawa kotun koli bisa hukunce hukuncen data yanke a ƙarar zaben gwamnonin ta bayyana cewa hukuncin ya ƙara nuna tabbacin cewa ɓangaren shari’a na cin gashin kansa.

Kungiyar Kwadago ta TUC tace gwamntin tarayya ta dakar da biyan karin albashi na Naira N35,000 da tayi alkawari tun a watan farko da ta biya sau 1 tak, duk kuwa da samun kudin shigar da za ta iya biya.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya umurci kwamandojin shiyyoyi da DPO na ƴan sanda su ƙara zage damtse a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.

Turkiyya ta lalata wurare 29 na kungiyar ‘yan ta’adda ta PKK a arewacin Iraki da Syria, a cewar Ma’aikatar Tsaro kasar.

Amurka ta ce ta kai hari kan ‘yan tawayen Houthi don karya ƙungiyar.

Hukumar OCTRIS ta sanar da kame kilo dubu 8 na miyagun kwayoyi a Nijar.

Juventus ta tattauna da ɗan wasan Ingila Jordan Henderson, kan dawo wa wurinta zaman aro daga Al-Ettifaq.

EPL: Burnley da Luton sun tashi 1:1 a wasan jiya.

Laliga: Deportivo ta sami nasara akan da ci 3:2 a wasan jiya.

Bundesliga: Bayern Munich ta sami akan Hoffenheim da ci 3:0 a wasan jiya.
Sakonnin Labarai yana zuwa muku ne a koda yaushe daga me cirowa IBRAHIM SUNUSI ISAH (S. WAYAU ZAZZAU) domin sanin abubuwan dake faruwa a gida da KETARE.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *