Biyo bayan baraɓaɓiyar harƙallar biliyoyin kuɗaɗen da ake bincike a Shirin NSIP, Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shirin, wanda aka sani da Shirin Raba Tallafin Marasa Galihu, wanda Hukumar NSIPA ke jagoranta, ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji, Jinƙai da Rage Raɗaɗin Talauci.
Alfijir labarai ta rawaito, Shugaba Tinubu ya bada umarnin cewa duk wasu ayyukan Hukumar NSIPA ciki har da raba tallafi, biyan kuɗaɗe, ayyukan haɗin-guiwa da rajistar marasa galihu a dakatar da su, sai bayan kammala binciken da ake yi tukunna.
Cikin wata sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya fitar a ranar Juma’a, tace sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya ce, dakatar da aikin ya zama wajibi, domin a samu damar gudanar da bincike sosai da sosai.
Ayyukan hukumar ya ƙara cin karo da fuskantar tazgaro bayan fallasa yadda fakatacciyar Ministar Agaji Betta Edu ta bada umarni aka zuba tsabar kuɗaɗe har Naira miliyan 585.2 cikin aljihun wata ma’aikaciya.
“An dakatar da dukkan shirye-shirye huɗu da NSIP ke yi, waɗanda suka haɗa da Shirin N-Power, Raba wa Masara Galihu Kuɗaɗe da Shirin Ƙarfafa wa Masu Ƙananan Sana’o’i da kuma Shirin Ciyar da Ɗalibai.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl