‘Yan sanda sun kama mutane 2 da satar janareto da batirin Solar masallaci

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Asabar.

Hassan ya ce a ranar Alhamis din da ta gabata, bisa samun sahihan bayanai, jami’an ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin tare da kai shi ofishin unguwar Sabon Garin da ke karamar hukumar Hunkuyi a jihar.

Hassan ya ce, “An kama wanda ake zargin ne da laifin sata a cikin masallacin.”

A cewarsa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin satar janareta da batir mai amfani da hasken rana a kauyen Hunkuyi da kauyen Nahuce a cikin masallacin su.

“Wanda ake zargin ya ci gaba da cewa ya sayar da kayan da ya sata ga wanda ake zargi na biyu .

“An gano wasu abubuwan da dama, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike,” in ji Hassan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *