Kwankwaso Da Ganduje Sun Magantu Kan Tayin Shiga Zauren Dattawa da Gwamna Abba Ya Kafa.

IMG 20240116 113308

Tsofaffin gwamnonin jihar Kano guda biyu, Sanata Rabiu Kwankwaso da magajinsa, Dr Abdullahi Ganduje, sun amince da yin aikin ba da shawara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ta majalisar dattawan Kano.

Alfijir labarai ta rawaito anar Lahadin da ta gabata idan zaku tuna gwamnan Kano ya sanar da kafa majalisar dattawan Kano, wanda ya hada da dattawan jihar masu rike da mukamai da kuma tsoffin jami’an gwamnati, wadanda ‘yan asalin jihar ne don zama masu ba shi shawara.

A tattaunawar LEADERSHIP, da Shugaban ma aikatan Ofishin Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC Muhammad Garba ya ce, yana da sha’awar cigan Jihar, don haka kafa majalisar a matsayin abin maraba ne idan ba a siyasantashi ba.

Ya kara da cewa da irin nasarorin da Ganduje ya samu ta fuskar ci gaban bil’adama da samar da ababen more rayuwa a lokacin da yake gwamna, ya nuna cewa yana da muradin jihar a zuciyarsa.

Hakazalika, jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta ce shugabanta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, zai yi aiki a majalisar da aka gabatar.

Jam’iyyar ta ce Kwankwaso ya biya hakkinsa wajen ci gaban jihar, kuma zai tabbatar da dorewar abubuwan da ya gada domin amfanin al’ummar Kano da Najeriya.

A nasa bangaren sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP na kasa, Yakubu Shandam, ya bayyana kundin tsarin mulkin majalisar ba da shawara ta Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a matsayin abin yabawa ne.

“Abin farin ciki ne. Idan sauran gwamnonin za su yi koyi da haka, Nijeriya za ta ci gaba.

“Abba Gida-Gida yana son ci gaban jihar Kano kuma idan ya samu shawarwari daga shugabannin da suka gabata na jihar zai fi kyau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *