Sanata Aliero ya Magantu Kan Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Da Aka Yi

IMG 20240118 121833

Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Sanata Adamu Aliero ya bayyana cewa rufe kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar ya na yi wa ‘yan Arewa a ita kan ta Arewar mummunar illa.

Alfijir labarai ta rawaito Aliero ya ce rufe kan iyakar ya jefa ɗimbin ‘yan Arewa cikin matsananciyar rayuwar ƙunci.

Aliero wanda ke wakiltar Shiyyar Kebbi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana haka yayin ganawar da aka yi da shi da gidan talabijin na Arise TV, da safiyar Laraba.

Najeriya ta kulle dukkan kan iyakokin ta da Jamhuriyar Nijar a cikin watan Agustan 2023, bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohammed Bazoum, suka ɗora Janar Abdourahmane Tchiani kan mulki.

Haka kuma Najeriya ta yanke wutar da ta ke bai wa Nijar, duk dai a matsayin takurawa da takunkumin da zai sa sojoji su sauka daga mulki, amma abin bai yi nasara ba.

Mazauna yankunan da ke kan iyakokin ƙasashen biyu sun sha kokawa dangane da yadda harkokin kasuwanci a yankunan suka taɓarɓare tun bayan rufe kan iyakokin.

Jihohin da suka haɗa kan iyaka da Nijar sun haɗa da Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa da kuma Yobe da Barno.

Waɗannan jihohi bakwai sun haɗa iyakoki da yankunan Sosai, Tahou, Maraɗi, Zindar da kuma Diffa na Jamhuriyar Nijar.

Ƙuncin Rayuwa Bayan Rufe Kan Iyakoki:

Sanata Aliero ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta duba lamarin, ta gaggauta buɗe kan iyakokin domin ta sauƙaƙa wa al’ummar da ta ke mulki.

“Rufe kan iyakokin Najeriya da Nijar ba shi da wani tasiri ga tsarin harkokin diflomasiyyar Najeriya, matsawar abin da zai haifar sai ƙara wa ‘yan Najeriya shiga cikin ƙuncin rayuwa.

“Saboda lamarin ya shafi kasuwanci a Kano, Zamfara, Katsina, Jigawa, kai har ma da Kaduna, Yobe da Barno.”

Ya tunatar cewa ‘yan majalisar waɗannan yankuna sun yi kiraye-kirayen a buɗe iyakokin saboda a sauƙaƙa wa al’ummar yankin su daga halin ƙuncin da suke ciki, amma aka yi biris da su,” cewar Aliero.

Sanatan ya ce ‘yan Arewacin Najeriya na da alaƙar addini ɗaya, al’adu iri ɗaya da kuma kyakkyawar alaƙa ta auratayya tsakanin su. Ya ce Turawan mulki ne su ka raba yankin biyu.

Ya ce shi dai bai ga wani aiki da hankali a rufe kan iyakokin Najeriya da Nijar wanda aka yi ba.

Ya ce kama daga nan Najeriya har cikin Nijar da Burkina Faso jama’a na fama da matsanancin ƙuncin rayuwa sakamakon rufe kan iyakokin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *