Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa.
Alfijir labarai ta rawaito wasu shugabannin kungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar da batun kama Bodejo a yau Talata.
Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.
Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.
A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani
Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V