Labari Mai Dadi! Wani Dan Tiktok Ya Bada Gudummawar Sabuwar Mota Ga Hukumar Hisbah Ta Kano

Screenshot 20240307 111949 com.whatsapp edit 10536315170266

Wani dan Tiktoker mai suna Aminu J Town ya baiwa hukumar Hisbah ta jihar Kano kyautar mota a matsayin gudunmawar hukumar yaki da karuwanci da lalata a jihar.

Alfijir labarai ta ruwaito cewa Mista J Town ya bayar da tallafin ne a ranar Talata bayan ya yi tattaki daga Jos, jihar Filato domin kai motar.

Motar, Toyota Sienna Saloon, an rubuta sunan hukumar Hisbah.

Da yake mika motar ga kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, mai bayar da tallafin, Mista J Town ya yi kira ga sauran jama’a da kungiyoyi da su zakulo bukatun hukumar ta Hisbah tare da taimakawa hukumar, idan ya cancanta.

Ya kara da cewa akwai shirin bayar da karin motoci biyu da babura domin saukaka ayyukan hukumar.

Da yake karbar motar, babban jami’in Hisbah CG Sheikh Daurawa, ya mika godiyarsa ga wadanda suka bayar da gudummawar da tawagarsa bisa wannan kyauta.

A nasa jawabin mataimakin kwamandan kungiyar, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya dace da lokaci kuma yana da muhimmanci ga ayyukan hukumar.

Ya kuma yabawa ‘yan Tiktokers sannan kuma ya ja hankalin ‘yan Kano masu kishin kasa kan bukatar tallafawa hukumar.

Daily News 24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *