Khalifa Sanusi II Ya Fashe Da Kuka Lokacin Da Yake Jawabin Ta’aziyyar Rasuwar Herbert Wigwe

Screenshot 20240307 134314 com.facebook.katana edit 3196096952636

Daga Aminu Bala Madobi

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fashe da kuka a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron karrama marigayi Herbert
Wigwe, tsohon shugaban rukunin kamfanin Access Holdings Plc.

Alfijir labarai ta rawaito da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka halarci taron bikin karrama marigayin mai shekaru 57, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Sarki Sanusi ya ce ya yi zaton zai riga Herbert mutuwa.

” A nawa lissafin na yi zaton zan riga Herbert mutuwa, amma sai gashi ya tafi ya barmu a duniya.

Bayan haka da sarki Sanusi ya bayyana yadda marigayi Herbert ya tsaya masa tsayin daka a lokacin da gwamnatin Kano ta rantse sai ta ga bayan sa a sarautar Kano.

” A lokacin da na tabbatar ba makawa sai za a cire ni daga sarautar Kano, na kira shi na ce masa, Herbert, sai dai fa ayi hakuri amma babu makawa za a tsige ni daga sarautar Kano.

” A lokacin da aka sanar da tsige ni, da karfe tara na safe kafin 12 na rana, ya aiko da jirgin sama, na saka iyalaina zuwa Legas.

” Da suka sauka Legas, ya ajiye a Otelsaga baya kuma ya saka su a gida. Ya ce min duk abinda nake so yana nan tare da kai.

Bayan haka Sarki Sanusi ya bayyana yadda Herbert ya taimaka masa kan harkokin kuɗaɗensa na ajiya da na asusun ƴaƴan sa na karatu da sauransu.

Premium Times Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

One Reply to “Khalifa Sanusi II Ya Fashe Da Kuka Lokacin Da Yake Jawabin Ta’aziyyar Rasuwar Herbert Wigwe”

  1. Kamata yayi dayaje Tudun Biri yakwana can yana kukan mutuwar yan’darika ba mutuwar kafiri ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *