Gwanan Kano Yayi Allah Wadai Da Yadda Ake Gudanar Da shirin Ciyarwar Ramadan A Wasu Wurare A Kano.

FB IMG 1711170717298

“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba,

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa kan shirin ciyarwa na watan Ramadan da ake yi a cikin babban birnin Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.

Gwamnan ya ce ya ji takaicin shirin a lokacin da ya kai ziyarar bazata daya daga cikin cibiyoyin ciyar da abinci da ke Gidan Maza, karamar hukumar Municipal.

Gwamna Yusuf ya kuma nuna rashin jin dadinsa da yadda masu gudanar da shirin ke gudanar da ayyukansu, wadanda ya ke ganin suna hana wadanda suka ci gajiyar shirin.

“Ba za mu amince da rashin gaskiya da almubazzaranci da dukiyar al’umma ba, ya zama wajibi a lura da cewa kudaden da aka ware don wannan shiri an tsara su sosai a kowace cibiya” Gwamnan ya yi gargadin.

Gwamnan ya gudanar da ziyarar ne biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna nakasu wajen gudanar da shirin ciyarwa a cibiyoyi daban-daban na babban birnin.

FB IMG 1711170739518
📸 Abba Kabir Yusuf
FB IMG 1711170713949
📸 Abba Kabir Yusuf

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *