Anyi Garkuwa da ɗaliban ne a kauyen Gidan Bakuso dake ƙaramar hukumar Gada a lokacin da suke shiga dakunansu domin gujewa harin da aka kai wa al’umma makonni biyu da suka gabata.
Alfijir labarai ta rawaito an sace Almajiran ne sa’o’i kaɗan kafin bikin yaye jami’an tsaro da jihar Ta kirkiro domin yaki da ‘yan fashi.
Malamin makarantar Tsangaya da ke Gidan Bakuso, Liman Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’umma da misalin karfe 1:00 na safe, inda suka harbe mutum daya sannan suka yi awon gaba da wata mata.
Maigidan ya kara da cewa: “Lokacin da suke barin garin, sai suka hangi dalibanmu suna rugawa zuwa dakunansu a lokacin ne sukayi Garkuwa dasu


Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk