Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro a jihar Kano sun gano wani rahoton sirri da ke nuna cewa wasu bata gari na shirin kaddamar da tarzoma a muhimman wurare da suka hada da majalisar dokokin jihar da wasu gine-ginen gwamnati.
Alfijir labarai ta rawaito kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ‘yan sandan Kano.
Ya ce jami’an tsaro na hadin gwiwa za su rika gudanar da bincike gida-gida domin bankado duk wanda ke tunanin ya fi karfin hukuma.
CP Mohammed Usaini Gumel ya ce hukumomin tsaro za su tsaya tsayin daka wajen bin doka, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bin umarnin kotu.
Ya kuma baiwa jama’a tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma baki daya.
CP Mohammed Usaini Gumel ya bukaci jama’a da su yi kokarin bayar da hadin kai da nufin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa an yi zanga-zanga a Kano, inda ya ce ba gaskiya ba ne, kuma jita-jita ce ta wasu bata gari da ke da mugun nufi ga ci gaban jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL